Gwamnatin Ghana za ta rufe shagunan baki a kasarta

ghana Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Shugaban Ghana, John Attah Mills

Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Ghana za ta rurrufe duk shagunan da 'yan kasashen waje ke sayar da kayayyakinsun.

Dokar Kasar Ghana dai ta ba 'yan kasar ne kawai 'yancin sai da kaya a tebur da talla da kuma sayarda kayayyaki a kananan shaguna a unguwanni ko a cikin kasuwa.

Dokar ta ce duk dan kasar wajen da ke san sai da kayayyaki a unguwanni ko a cikin gari ti las ne ya ajiye akalla dala dubu dari 3 kuma ya dauki 'yan kasar Ghanan akalla 10 aiki.

Sai dai kuma a shekaru ashirin din da suka wuce dubban 'yan kasar waje-- yawancin 'yan kasar China da 'yan Najeriya- sun yi ta harkokin kasuwancinsu ba tare da cika wadannan sharuda ba.

Da alama matakin da gwamnatin Ghanar ta dauka ya sabawa dokokon ECOWAS wadanda suka ba duk wani dan kasashen kungiyar 'yancin kasuwanci da walwala a yankin.

Matakin da gwamnatin Ghanan ta dauka ya biyo bayan korafin da 'yan kasar suke yi ne shekara da shekaru kan cewa 'yan kasashen wajen sun toshe masu hanyar samun abincin a kasarsu.

Karin bayani