'Yan Ansarud Deen 'yan ta'adda ne —Ministar Mali

Wani dan kungiyar Ansarud Deen yana kabbara yayin da suke rusa wani hubbare Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani dan kungiyar Ansarud Deen yana kabbara yayin da suke rusa wani hubbare

Mayakan kungiyar masu zafin kishin Islama ta Ansarud Deen a Mali sun rusa mashigin wani masallaci wanda aka gina tun karni na goma sha biyar a Timbuktu, a ci gaba da rusa gine-ginen tarihi na birnin da suka fara tun ranar Asabar.

Wadansu daga cikin mazauna birnin dai sun yi ta rusa kuka yayin da ake rushe kofar shiga daya daga cikin masallatai uku masu dadadden tarihi a kasar ta Mali.

Babbar mai shigar da kara ta Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya, Fatou Bensouda, ta kwatanta al'amarin da aikata laifuffukan yaki, sannan ta yi barazanar gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a gaban kotun ta duniya.

A wata hira da ta yi da Sashen Faransanci na BBC, Ministar Al'adu ta kasar ta Mali, Fadima Toure Diallo, ta yi Allah-wadai da rushe-rushen.

“Suna nan suna kai hare-hare a kan hubbaren waliyyai da dama da kuma dukannin wuraren tarihi na wannan gari, wanda birni ne da Majalisar Dinkin Duniya ta hannun [hukumarta mai kula da al’adu,] UNESCO, ta baiwa matsayi na musamman a [jerin wurare masu daddaden tarihi.

“Abin da ke faruwa yana da ban takaici: Tumbuktu, gari ne da ya yi fice, kuma akwai waliyai dari uku da talatin da ke da hubbaren su a can”.

Minista Fadima Toure ta kuma bayyana masu fafitikar na kungiyar Ansarud Deen da cewa 'yan ta'adda ne:

“’Yan ta'adda ne; mutane ne wadanda ba su da imani ko kadan, kuma ba sa bin doka.

“Suna fakewa da sunan wani addini domin su lalata wurare masu muhimmanci, amma mu a nan Mali ba mu san irin wannan salon addinin da suke bi ba ko kadan”.

Karin bayani