Pena Nieto ya lashe zaben shugaban kasar Mexico

Enrique Pena Nieto Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Enrique Pena Nieto

Sakamakon zaben kasar Mexico na farko a hukumance, na nuna cewa dan takarar jamiyyar adawa Enrique Pena Nieto, ya yi wa abokan kararawarsa fintinkau.

Sakamakon wanda ba gaba daya ya shigo ba, ya nuna Mr Pena Nieto na jamiyyar PRI na kan gaba da kusan kashi 38 cikin dari.

Dan takarar jamiyyar PRD mai raayin sauyi Andres Manuel Lopez Obrador shi ne na biyu, yayinda dan takarar jamiyya mai mulki PAN ke mataki na ukku.

Duk da fargabar yiwuwar tashin hankali a wasu jihohin kasar da gungun masu safarar miyagun kwayoyi suka mamaye, an gudanar da zaben a mafi akasarin biranen kasar cikin kwanciyar hankali.

Karin bayani