Shugaban Nigeria ya ce ba-sani-ba-sabo kan cin hanci

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan

Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa tana sanyin-jiki wajen aiwatar da rahoton da majalisar wakilan kasar ta gabatar, wanda a cikinsa aka zargi wasu 'yan kasar da yin cuwa-cuwa a harkar tallafin mai.

Gwamnatin ta ce ba za ta saurara ba wajen ganin an hukunta dukkan wadanda aka samu da laifi.

Shugaban Najeriyar, Goodluck Jonathan, ya sha alwashin cewa babu wani dan gaban-goshi ko shafaffe da man da gwamnatinsa za ta saurara masa, muddin aka same da aikata laifi.

Tuni dai kwamitin ladabtarwar Majalisar Wakilan kasar ya fara bincike a kan zargin karbar rashawar da ake yi wa tsohon shugaban kwamitin bincike a kan yadda gwamnati ta gudanar da harkar tallafin mai, wato Honourable Faruk Lawan.

Karin bayani