Shugaban bankin Barclays na Birtaniya ya yi murabus

Bob Diamond
Image caption Bob Diamond

Shugaban gudanar da katafaren bankin Barclays na Birtaniya, Bob Diamond ya yi murabus bayan sukan da ya sha akan zargin da aka yi wa bankin na yin cogen kudin ruwa.

Bankin Barclays dai ya fuskanci suka tun bayan da ya amsa cewar ya yi kokarin yin coge wajen saka kudin ruwa da bankin ke cazar wasu bankunan, ko yake biya.

A jiya ma shugaban hukumar gudanarwar bankin Marcus Agius , ya sauka daga kan mukaminsa.

BBC dai ta gano cewa, Bob Diamond ya yanke shawarar yin murabus ne bayan gwamnan babban bankin Ingila, Sir Mervyn King da kuma shugaban hukumar dake sa ido akan cibiyoyin kudi na Birtaniya, Lord Turner sun ce masa abinda ya kamata shi ne, ya yi murabus. Wakilin BBC ya ce, shi dai Bob Diamond ya ce, akwai siyasa a cikin matsin lambar da aka yi masa yayi murabus, kuma tuni 'yan siyasa ke yin marhabun da yin murabus din da yayi.

Bob Diamond dai ya ce, matsin lamba a kan wannan batu ka iya yin illa ga bankin na Barcklays.