Majalisar dinkin duniya ta ce an cimma uku daga cikin muradun karni

Tambarin Majalisar dinkin duniya
Image caption Tambarin Majalisar dinkin duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an cinma uku daga cikin muhimman muradun sabon karni da aka debar ma wa'adi.

A rahotonta na shekara, Majalisar Dinkin Duniya ta ce an samu ci gaba wajen kokarin rage talauci, da inganta rayuwar mutane dake zaune a anguwannin marasa galihu, da kuma samar da tsabtataccen ruwa.

Shugabannin duniya sun amince da muradun karnin 8 ne a wajen wani taron koli a birnin New York a shekara ta dubu biyu.

Sun nufi mayar da hankali kan kawar da fatara da ilmi da daidaiton jinsi da kula da lafiyar yara da mata masu juna biyu da kyautata muhalli da rage ciwon Aids da kwayar cutar dake haddasa ta ta HIV, da kuma abinda ake kira kawancen duniya kan ci gaba.

To amma Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, Ban Ki-Moonyayi gargadi game da sakaci, yana mai cewar bai kamata a bar rahoton ya zama wani dalili na jan kafa ba.

Ya ce hasashe ya nuna cewar nan da 2015 mutane fiye da miliyan 600 za su rasa samun tsaftataccen ruwa, sannan kusan biliyan daya za su rayu da kasa da dan abinda ya dara wa Dola daya a rana, iyaye mata kuma za su ci gaba da mutuwa a wajen haihuwa, yara kuma su mutu daga cututtukan da za a iya kare kai daga kamuwa da su.