An kona rugagen filani a jihar Pilato

jos
Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga Jihar Filato a Nijeriya na cewa ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula nan da can a 'yan kwanakin nan inda ko a yau rahotanni suka ce an kona gidajen Fulani makiyaya da dama a yankin Barkin Ladi.

Lamarin dai ya biyo bayan wasu kashe-kashe ne a yankin na Barkin Ladi da kuma yankin Riyom a 'yan kwanakin nan, inda mutane akalla hudu suka rasa rayukansu, ciki har da wani dan siyasa da iyalansa biyu.

Kawo yanzu dai ba a san ko kone-konen na yau na da nasaba da wadancan lamurra ba, sai dai kuma da ma jihar ta Filato ta dade tana fama da rigingimu.

Bisa dukkan alamu dai, ba a soma hango karshen matsalar tsaro da jihar ta Filato da ma wasu jihohin Nijeriya ke fama da su nan kusa ba, ganin yadda lamarin ke ci gaba da ta'azzara da kuma sauya salo, duk da ikirarin da hukumomin kasar ke yi na kokarin maganceta.

Karin bayani