Shugaban Bankin Barclays zai amsa tambayoyi

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Bod Diamond, shugaban bankin Barclays da yayi murabus

Tsohon shugaban bankin Barclays, daya daga cikin manyan bankunan Burtaniya, zai fuskanci tambayoyi daga wani kwamitin majalisar wakilai ranar Laraba game da badakalar murde alkalumman kudin ruwan da ta jawo masa ya rasa kujerarsa.

A ranar Talata ne Bob Diamond ya ajiye aiki bayan kakkausar sukar da ta biyo bayan laifin da bankin Barclays ya yi na boye hakikanin kudin ruwan da ya ke biya kan basussukan da bankin kan karba daga sauran bankuna, abinda ya sa aka ci bankin tara mai dimbin yawa.

Wakilin BBC yace ana da alamun za'a kwashi 'yan kallo tsakanin mutumin da a da ake kallonsa a matsayin gwarzo abin koyi a sana'ar aikin banki da kuma kwamitin 'yan majalisar da ke fargabar wannan badakalar ta bata sunan London, a matsayinta na cibiyar hada-hadar kudi.

Bankin na Barclays dai ya amsa cewar ma'aikatansa sun yi muna-muna kan yawan kudin ruwan ne tsakanin shekarun 2005 da 2009.

Karin bayani