An samu tashin 'bam' a Abuja

Wani wurin da aka kaiwa harin a kusa da birnin na Abuja

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Wani wurin da aka kaiwa harin a kusa da birnin na Abuja

Akalla mutum daya ne ya raunata bayan da wani abu da ake zaton bom ne ya tashi a kusa da wasu manyan shagunan sayar da kayan masarufi dake Abuja babban birnin Najeriya.

Bom din dai ya tashi ne a kusa da wani mashahurin shagon sayar da kayan masarufi da ake kira Banex Plaza dake Unguwar Wuse II dake birnin na Abuja.

Wannan abin da ake jin Bom ne dai ya tashi ne da misalin karfe tara na daren jiya lokacinda masu kasuwanci a wurin suka soma kimtsawa domin rufe shagunansu.

Wasu shaidu sunce an jefa abin mai fashewa ne a karkashin wata mota kuma ya tashi inda ya raunata mutum daya.

Tashin wannan abin da ake jin bom ne dai shi ne irinsa na biyu a unguwar ta wuse ii a cikin makonni biyu inda a ranar 23 ga watan jiya aka jefo wani abu mai fashewa daga cikin wata mota dake tafiya a bakin wani gidan rawa, abinda ya lalata motoci akalla shida.

Isar jami'an tsaro

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai ba a san ko wanene fashewar abin ta raunata ba amma dai ance an ruga da shi zuwa asibiti domin yi masa magani.

Wakilin BBC da ya je wurin dai, yace ko da ya isa jami'an tsaro sun riga killace wurin domin kokarin tattaro ababen da zasu taimaka musu wajen bincike adaidai lokacinda babban sufetan Y'an sandan kasar ya isa a can.

Shugaban hukumar bayarda agajin gaggawa ta kasar mai kula da yankin Abuja, Ishaya Chonoko ya shaidawa BBC cewar jami'an tsaro sun gano tare da kwance wani abu mai fashewar da aka dana dab da inda na farkon ya tashi.