Pakistan za ta sake bude iyakokinta ga NATO

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hillary Clinton

Pakistan ta amince ta sake bude hanyoyin isar da kayayyakin amfani ga dakarun NATO da ke Afghanistan bayan da Amurka ta ba ta hakuri bisa kashe sojin Pakistan 24 da dakarun Amurkan su ka yi.

Sakatariyar Hulda da Kasashen waje ta Amurka, Hillary Clinton, ta ce Amurka ta yi matukar nadamar lamarin da ya afku a watan Nuwamban bara.

Sai dai Amurkan ta ki amincewa da biyan kudin fito na dala dubu biyar ga dukkan akwatun kayan NATO guda da gwamnatin Pakistan din ta bukata.

Kodayake wakilin BBC a Islamabad ya ce yarjejeniyar za ta bai wa Amurka damar ba Pakistan tallafin soji da ya kai na kudi dala biliyan guda.

Karin bayani