An kona wani mutumi a Pakistan saboda zargin kona Alkur'ani

zanga Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga zanga a Pakistan saboda zargin yin sabo

Wani mutumi da aka zarga da sabo, an kona shi da ransa a Pakistan, kamar dai yadda 'yan sanda suka ce a yankin.

Suka ce dubban mutane ne suka mamaye ofishin 'yan sanda a Kudancin Lardin Punjab, inda ake tsare da shi.

Akwai rahotannin da ba a tabbatar ba da ke cewa mutumin yana da tabin hankali.

Mutumin da ake zargin na tsare ne a hannun 'yan sanda, to amma koda shingen rodin da yake bayansa bai iya kare shi ba.

'Yan sanda sunce ba su data yi a lokacin da dubun dubatar masu zanga zanga suka afka suka janyo shi.

An kona shi da ransa -a inda aka yi zargin ya kona wani Al-Qur'ani mai girma.

Zargin yin sabo zai iya zama hukunci kisa a nan, kamar yadda ma'aikatan kare hakkin bil adama na Pakistan suka ce.

Yayinda 'yan sanda suka ceci wasu da ake zargi sunce akwai yiwuwar jami;'ai su bar masu zanga zanga su ci karensu ba babbaka.

Karin bayani