Masana kimiyya sun gano wata sabuwar kwayar zarra

scientist Hakkin mallakar hoto fraunhofer igb
Image caption Masu binciken kimiyya

Masana kimiyya dake aiki a wani dakin bincike dake Switzerland sun ce sun gano wani sabon bangaren kwayar zarra.

Masana kimiyyar sun ce, abinda suka gano ya yi daidai da bangaren kwayar zarra da suka kira Higg Boson wadda aka shafe shekaru 45 ana kokarin gano wa.

Wakilin BBC yace "wannan binciken ana yinsa ne saboda a samo amsar wasu bayanai dangane da yadda kwayar zarra ke aiki.

Farfesa Peter Higgs wanda yayi hasashen kasancewar wannan bangare na kwayar zarra a shekara alif dari tara da sittin da hudu, yace ya zubda hawaye yayin da aka bayyana sakamakon wannan bincike.

Karin bayani