Mutum ne ya jawo masifar nukiliyar Japan

Hakkin mallakar hoto AFP

Wani rahoto kan masifar da ta faru a tashar makamashin nukiliya ta Fukushima a Japan ya ce masifa ce da dan adam ya jawo, wadda ya kamata a ce an hango an kuma hana ta afkuwa.

Shugaban kwamitin da ya gudanar da binciken ya ce kura-kurai da dama da aka tafka ya sa tashar bata shirya tinkarar girgizar kasa da ambaliyar ruwa ta Tsunamin da suka afkawa kasar a watan Maris na bara ba.

Kiyoshi Kurokawa ya ce cikin watanni shidda ne su ka yi kokarin hada rahotan, kuma duk da cewa kankanin lokaci ne, sun gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Kakakin majalisar dokokin kasar ta Japan, Takahiro Yokomichi, ya ce za su yi amfani da sakamakon binciken nan gaba wajen shirya tsarin makamashin kasar.

Karin bayani