Shugabannin tsaro a Najeriya na ta kokarin daidaita al'amura a kasar

Kanar Sambo Dasuki Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Kanar Sambo Dasuki

Mai baiwa shugaban Nigeria shawara ta fuskar tsaro Kanal Sambo Dasuki mai ritaya ya gana da wasu bangarorin masu ruwa da tsaki ta bangaren tsaro a jihar Kano dake arewacin Nigeria.

Mai bada shawarar ya ce yana kai ziyara jihohin kasar ne, musamman wadanda ke fsukantar mastalar tsaro dan duba inda gwamnatin kasar zata kara taimakawa gwamnatocin jihohin a magance matsalolin da ake fuskanta.

Sai dai mai bada shawarar ya ki amincewa ya yi magana da yan jaridu a yayin ziyarar.

A waje daya kuma, wasu rahotanni daga Kano sunce an ji karar fashewar wasu abubuwa a unguwar Kadawa dake gefen unguwar jan bulo a birnin da yammaci.

Mazauna yankin sun ce sun ji karar fashewar abubuwan ne , yayin da wani da ke wajen ya ce abin ya faru ne a wani gida.

Kawo yanzu dai hukumomin tsaron jihar ba su kai ga karin bayani ba, haka kuma babu wasu karin bayanai dangane da illar da lamarin ya haifar.

Bugu da kari kuma a kokarin lalumo hanyoyin warware matsalolin tsaron da suka addabi wasu sassa na arewacin Najeriya ,shugaban yansandan Najeriya M D Abubakar ya kai wata ziyara jahar kaduna inda ya gana da gwamnan jahar da kuma wasu manyan jamian tsaron jahar wacce ita ma ke fuskantar kalubalen tsaron.

A ziyarar dai shugaban na yansandan na Najeriya ya bayyana cewa a yanzu suna kokarin shawo kan matsalar da ta addabi kasar ta tsaro haka kuma suna iya kokarin ganin sun magance kallon hadarin kajin da wasu a kasar ke yiwa yansanda.

Shugaban yansandan dai ya kai wannan ziyara jahar kaduna ne a yayin da aka wayi gari da jita jita da shaci fadin yiwuwar afkuwar tashin hankali,abinda ya haifar da guje gujen dauko yara daga makarantu da kuma hanzarin rufe shaguna.

Karin bayani