Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a kafa wa 'yan tawayen Mali takunkumi

Mayakan kungiyar Ansaruddin na Mali Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kwamitin Tsaro ya yi barazanar gurfanarwa a Kotun Miyagun Laifuka

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da kuduri, inda yake kiran a sanya takunkumi a kan mayaka masu kishin Islama a arewacin Mali, wadanda suka ragargaza hubbarori na tarihi masu yawa a birnin Timbuktu.

Kwamitin dai ya ja burki game da ba da goyon baya ga kafa rundunar kasashen Yammacin Afrika, don taimakawa wajen yakar 'yan tawayen.

A maimakon haka, tana bukatar karin bayani ne game da rundunar da kuma gurinta.

Kudurin ya kuma yi gargadin cewa duk wanda ke da alhakin rusa gine-ginen tarihi a Timbuktun, zai iya fuskantar gurfanarwa a gaban Kotun Miyagun Laifuka ta Duniya.

Kudurin na MDD dai ya nuna matukar damuwa da yadda ya ce barazanar 'yan ta'adda na karuwa a arewacin Mali da ma daukacin yankin Afirka kudu da Sahara.

Don haka kudurin ya yi kira ga kasashe mambobin majalisar su mika sunayen mutanen da ke da alaka da kungiyar Alka'ida don a sanya sunayensu a jerin mayakan kungiyar da Majalisar ta Dinkin Duniya ta kakaba wa takunkumi.

Ya yi Allah-wadai da yadda mayakan Ansar Deen suka rushe hubbarori, yana mai cewa hakan ya fada cikin hurumin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

Karin bayani