An tuhumi 'yan Najeriya da alaka da Al-Qa'ida

Kanar Sambo Dasuki mai ritaya Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Mai ba Shugaban Najeriya shawara a kan harkar tsaro, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya

An zargi wadansu mutane biyu 'yan Najeriya da alaka da kungiyar Al-Qa'ida da kuma diban mutane su kai su Yemen don a ba su horo.

Mutanen biyu, Olaniyi Lawal mai shekaru talatin da daya a duniya, da Luqman Babatunde mai shekaru talatin, sun musanta zargin a gaban wata kotu a Abuja, babban birnin kasar.

An tuhumi mutanen ne da karbar kudi daga reshen kungiyar Al-Qa'ida na Jaziratul Arab (AQAP) da kuma "yada manufofin" kungiyar.

A watan Fabrairun bana ne dai wata kotun Amurka ta yanke wa wani dan Najeriyar, Umar Farouk Abdulmutallab, hukuncin daurin rai-da-rai bisa tuhumar alaka da kungiyar ta AQAP.

Shi dai Umar Farouk Abdulmutallab ya amsa tuhumar da aka yi masa ta yunkurin tarwatsa wani jirgin sama ranar Kirsimatin shekarar 2009.

Masu shigar da kara sun ce malamin nan haifaffen kasar ta Amurka Anwar al-Awlaki, wanda dan asalin kasar Yemen ne kuma ake tunanin shi ne jagoran kungiyar ta AQAP, shi ne ya cusa wa Umar Farouk tsattsauran ra'ayin addini.

An kuma alakanta kungiyar Boko Haram a kasar ta Najeriya da wani reshe na daban na kungiyar ta Al-Qa'ida da ke arewacin Afirka.

An dai dora alhakin mutuwar daruruwan mutane a wasu hare-hare a arewacin kasar ta Najeriya a kan kungiyar ta Boko Haram. A cewar jami'an Amurka, mai yiwuwa kungiyar na musayar kudade da abubuwa masu fashewa da ma horo da kungiyar Al-Qa'ida a Yankin Magreb da kuma kungiyar Al-Shabaab.

Har yanzu dai kungiyar ta Boko Haram, wacce ta ce tana fada ne da nufin mayar da Najeriya kasar Musulunci, ba ta ce komai ba a kan wadannan zarge-zarge.

Sai dai kuma ya zuwa yanzu ba a nuna akwai dangantaka ba a tsakanin mutanen biyu--wadanda suka fito daga kudancin kasar--da Boko Haram mai tsuhe a arewacin kasar.

Takardun kotu dai sun ce an tuhumi Mista Lawal da Mista Babatunde da laifin karbar "kudade dalar Amurka da riyal na Saudi Arabia wadanda darajarsu ta kai naira miliyan daya daga kungiyar ta AQAP.

An kuma zarge su da laifin shirya amfani da kudin wajen "dauka da kuma jigilar sabbin mambobi zuwa wani sansanin horo da ke Yemen", abin da ya saba da dokokin Najeriya masu fada da ta'addanci.

Karin bayani