An kashe yan kishin Islama 9 a Pakistan

Hari a Pkistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption wata mota bayan harin bam a Pakistan

Jami'an leken asiri a Pakistan sun ce an kashe mutane tara wadanda ake zargin 'yan kishin Islama ne a kasar.

An dai kashe masu kishin Islamar ne a wani hari na makami mai linzami da aka harba daga jirgin saman Amurka wanda bai da matuka a yankin arewacin Waziristan dab da kan iyaka da Afghanistan.

Jiragen maras sa matuka na Amurka suna kai hari a kai a kai a yankunan da ake kyautata zaton mafakar 'yan kungiyar Taliban ne da al-qaeda.

An dai kai irin wadannan hare haren a kasar Afghanistan a kwanakin baya.

Karin bayani