Da wuya a yiwa Saif Gaddafi adalci

Saif Al-Islam Gaddafi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Saif Al-Islam Gaddafi

Wata Lauyar da kotun manyan laifuka ta Duniya ta nada domin taimakawa wajen kare Saif Al-Islam Gaddafi, dan marigayi Shugaban Libya, ta ce tsare ta da aka yi yayinda ta ke ziyartarsa a Libya ya nuna cewar ba za a yi masa shari'ar adalci ba a can.

A ranar litinin ne dai aka saki, Lauyar, Melinda Taylor yar Australia, da kuma abokan aikintga uku, bayan da aka tsare su har kusan tsawon wata daya.

Melinda Taylor ta ce matsayin lauyoyin kariya ne cewar ababuwan da suka faru a baya ga baki daya sun nuna cewar zai yi wuya a yiwa Saif Al-Islam Gaddafi shari'a a yanayi na rashin nunin adalci da son kai a kotunan Libya.

Hukumomi a garin Zintan na yammacin kasar, inda ake tsare da Saif Gaddafi, bisa zargin laifukan yaki, sun zargi Ms Taylor da sauran abokan aikin ta uku da yiwa sha'anin tsaron Libya karan tsaye.

Karin bayani