Moon ya bada shawarar rage masu sa ido a Syria

Ban ki Moon Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Moon ya bada shawara kan masu sa ido a syria

Yayinda ya rage makwanni biyu wa'adin aikin wakilan Majalisar Dinkin Duniya masu sa ido a Syria ya kare, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ba da shawarar a rage yawan wakilan da rawar da suke takawa.

Ban ki Moon ya fada a wani rahoto ga kwamitin sulhu na Majalisar dinkin duniyar cewa kamata ya yi wakilan su maida hankali ga al'amurran siyasa.

Rikicin dai na Syria ya dagule sosai inda kasashen duniya ke ta magana akai.

Mutane da dama dai sun rasa rayukansu a rikicin haka kuma ana asarar dukiya.

Karin bayani