Rasha da China za su dandana kudarsu! Inji Clinton

Taron Kasashe abokan Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron Kasashe abokan Syria

Faransa ta tabbatar cewa wani janar na kasar Syria daga wani gida mai karfin fada a ji dake kusa da shugaba Assad ya bar Syria.

Hakan kuwa na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu kasashe ke taro akan kasar ta Syria a birnin Paris.

Kuma a jawabin da tai a wajen taron sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta yi kira ga dukkan kasashe da su tabbatar cewa Rasha da China za su dan-dana kudarsu bisa goyan bayan da suke ba Shugaba Bashar al-Assad..

Mrs Clinton ta ce tarnakin da kasashe biyun ke kawowa a kokarin da ake na kawo karshen rikicin da ake a Syria abu ne da baza a ci gaba da lamunta ba.

Shugaban Syria Bashar Al Asaad na cigaba da fuskantar matsin lamba da kuma kauracewa daga aminansa, abinda kuma ke kara karfafawa 'yan adawa kwarin gwiwa a yinkurinsu na neman galaba akan gwamnatinsa.

A yanzu haka dai wani babban mutum wanda ke da alaka ta kut kut da iyalan gidan Al Assad, wato Janar Manaf Tlass ya juyawa shugaban Syri'ar baya.

Shugaba Bashar Al Assad ya dogara ne ga aminansa da kuma mukwarabbansa don cigaba da jan ragamar kasar, a don haka canza shekar da Janar Manaf Tlass ya yi, babban cikas ne ga shugaba Assad.

Janar Tlass dai ya raba gari ne da shugabannin Syria ne sakamakon yadda ake amfani da karfi wajen murkushe masu zanga zanga.

Kasashe fiye dari daya ne ke halarta taron akan Syria wanda ake yi a birnin Paris.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta shaidawa mahalarta taron cewar ya kamata ayi kamun kafa a wajen kasashen Rasha da China don su daina goyon bayan shugaba Assad.

Babban kalubalen da mahalarta wannan taron ke fuskanta shine kasancewar Rasha da China basu halarta ba, kuma sune ake neman hadin kansu don kawo karshe zubar da jini a Syriar

Karin bayani