An samu tashin hankali a kauyen Kukuru na Filato

jos
Image caption An dade ana zaman dar dar a Jos

Rahotanni daga karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato na cewa sabon fada ya barke a kauyen Kakuru da wasu wurare dake kewaye da shi inda aka yi ta'adi mai dimbin yawa.

Hukumomin tsaro dai sun bayyana cewa an samu hasarar rayuka a lamarin amma basu kai ga tantance adadin hasarar ba, sai dai kuma an yi kaca-kaca da kauyen.

Dama dai an dade ana samun rikici tsakanin Fulani da kabilar Berom a yankin da kan yi sanadiyar hasarar rayuka da dukiya.

Bayanai daga yankin na Barkin Ladi dai na cewa tun bayan da aka samun tashin hankali a yankin a ranar Talata da ta gabata inda Fulani suka zargi jami'an tsaro da kona masu gidaje masu yawan gaske da kuma tarwatsa su, zaman dar-dar ya karu a yankin matuka.

Jiya (Juma'a) ne kuma sai lamarin ya dada kamari bayan da al'umar Berom suka zargi Fulani da lalata masu amfanin gona abinda ya kai ga har suka yi zanga-zanga don nuna adawa da hakan a yau kuma tashin hankali barke inda Fulani suka zargi Berom da far masu.

Jami'in tsare-tsare na kungiyar agajin Krista ta Stefanos Foundation, Injiya Mark Lipdo, ya shaida mani ta wayar tarho cewa Fulani ne far wa mazauna yankin, amma kuma Sakataren kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Muhammad Nura Abdullahi ya ce Berom ne suka far wa Fulani da safiyar yau tare da daurin gingin jami'an tsaro, lamarin kuma ya ta'azzara ya zama mummunan tashin hankali.

Koda yake dai ana samun bayanai masu cin karo da juna kan musabbanin mummunar tashin hankalin, to amma abinda yake a fili bisa bayanai shi ne, kauyen na Kakuru an yi masa mummar illa, inda inda kakakin rundunar 'yan sandan jihar Filato, Abuh Emmanuel ya tabbatar da cewa kusan baki dayan kauyen an yi kaca-kaca da shi kana yace suna zargin aikin Fulani ne, zargin da Fulanin ke musantawa.

Karin bayani