Merkel da Hollande sun tattauna a birnin Reims

merkel Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Angela Merkel ta Jamus da Francois Hollande na Faransa

Shugaban Faransa, Francois Hollande da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel na wata ganawa a Reims dake arewacin Faransa, domin tunawa da kawancen da kasashen biyu suka kulla, wanda ya kafa harsashin kungiyar tarayyar Turai.

A yau ake cika shekaru hamsin da Shugaba Charles de Gaulle na Faransa, da Konrad Adenauer na Jamus ta Yamma suka yi wata ganawa a matsayin wata alama ta sasantawa bayan yakin duniya, lamarin da Angela Merkel ta kira bude sabon babi.

Shugabannin biyu sun halarci taron addu'o'i a cocin garin na Reims.

Kafin ganawar ta yau dai an lalata kaburburan wasu sojojin Jamus su arba'in da aka kashe a lokacin yakin duniya na farko, a wata makabarta ta sojoji dake kusa da garin na Reims.

Karin bayani