Mutane dari sun mutu sakamakon ambaliya a Rasha

rasha
Image caption Ruwa kamar da bakin kwarya ya janyo ambaliya a Rasha

Ruwa kamar da bakin kwarya a kudancin Rasha ya haddasa ambaliya, da kuma zabtarewar laka, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane dari a yankin Krasnodar.

Lamarin ya kuma janyo dakatar da jigilar danyen mai ta jirgin ruwa daga tashar jiragen ruwar Novorossissk, wadda ita ce mafi girma a kan tekun Bahar Aswad, aka kuma katse hanyoyin zirga zirga a yankin.

Wasu shaidu na cewa mutane da dama na barci lokacin da ruwan yayi ta malale tituna da gidaje, lamarin da ya haddasa aka shiga rudani.

Mutane da dama be suka tafka hasara sakamakon wannan ambaliyar.

Ga abinda wata yar garin Krymsk ke cewa"mun yi asarar kayayyakinmu, dukkan kadarorinmu, wannan abu ya girgiza mu".

Gwamnan yankin ya ce ruwan ya zo da matukar karfi, ta yadda ya rika yin awon gaba da hanyoyin mota.