ECOWAS ta yi kira ayi gwamnatin hadin-kasa

ECOWAS Hakkin mallakar hoto
Image caption Taron ECOWAS kan Mali

Shugabannin kasashen Yammacin Afrika sun yi kiran da a kafa gwamnatin hadin-kan kasa a Mali don kawo karshen rikicin siyasar da aka shafe watanni ana yi bayan mayakan 'yan kishin Islama da Abzinawa 'yan tawaye sun kwace yankin arewacin kasar.

Kungiyar kasashen yankin ECOWAS ta nemi a kafa gwamnatin hadin-kan kasar zuwa karshen wannan watan.

Haka nan kuma Kungiyar ta ECOWAS ta yi kira ga Kotun duniya mai bincike da hukunta miyagun laifuka ta binciki laifukan yakin da aka yi zargin an tafka a arewacin Mali.

Kungiyoyin 'yan tawayen sun kwace arewacin kasar ne lokacin yamutsin siyasar da ya biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a cikin watan Maris.

Karin bayani