Majalisar sojin Masar ta ce dole a yi amfani da hukuncin kotu

Majalisar dokokin Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Majalisar dokokin Masar

Majalisar sojin kasar Masar ta ce tilas ne a yi aiki da kundin tsarin mulkin kasar, bayan da sabon shugaban kasar, Muhammed Morsi ya yi watsi da wata shawarar da sojojin suka dauka na rusa majalisar dokokin kasar.

A ranar talata ne kakakin majalisar zai kira zaman majalisar dokokin bisa umurnin shugaba Morsi.

Sai dai kuma a wata sanarwar da ta fitar majalisar mulkin soji ta kasar ta ce ta rusa majalisar dokokin ne bisa kiyaye wa da hukuncin kotun kolin tsarin mulki ta kasar, kuma tilas ne kowa ya mutunta shi.

Tun da farko dai kotun kolin tsarin mulkin kasar ta Masar ta ce tilas ne a yi amfani da hukuncin nata, kuma ba a iya daukaka kara kansa.

Karin bayani