Najeriya: an tsaida kudin Hajjin bana

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Hukumar kula da alhazai ta Nigeria ta bayyana kudin aikin haji bana kuma ta ce kudin da manniyata zasu biya ya danganta ne kan shiyyar da suka fito.

Hukumar kula da alhazan ta ma ce zata fara jigilar maniyyata daga ranar goma sha takwas ga watan Satumba ta shekerar da muke ciki, yayin da za'a kamala jigilar cikin Octoba.

Hukumar alhazan Najeriyar tace, an samu karin kudin aikin Hajjin bana ne saboda karuwar kudin jirgin sama da kuma kudin masauki a birnin Makkah mai tsarki.