Wadanda suka mutu a rikicin Filato sun kai 84

Taswirar Najeriya
Image caption Jihar Filato ta yi kusan shekaru goma tana fama da rikice-rikice

Rahotanni daga Jihar Filato a arewacin Najeriya na cewa ana ci gaba da samun karin haske a kan adadin asarar rayukan da aka yi a tashin hankalin da ya auku a karshen mako, inda hukumomin tsaro suka ce mutane kusan casa'in ne suka rasa rayukansu.

An dai dade ba a samu al'amuran kashe-kashen jama'a a jihar ta Filato kamar wadanda aka gani a karshen makon ba, kuma tashe-tashen hankulan sun rutsa da kusann dukkan bangarori na al'uma, kama daga farar hula zuwa jami'an tsaro, da kuma wadanda ba a saba kashewa ko samun asarar rayukansu a al'amuran ba, wato 'yan siyasa; 'yan majalisun dokoki biyu ne dai suka gamu da ajalinsu.

Bayanai sun nuna cewa an samu karin gawarwakin mutane a wadansu kauyuka na karamar hukumar Barikin Ladi, inda wadansu rahotanni ke cewa an samu gawarwakin ne a wata majami'a yayin da wadansu kuma ke cewa a gidan wani malamin addinin Kirista, amma rundunar tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a jihar ta ce ba ta labarin samun gawarwaki a wani wuri mai nasaba da addini.

Kakakin rundunar, Kyaftin Mustapha Salisu, ya shaidawa BBC cewa "Da yake kauyukan wurin guda takwas ne an samu gawarwaki kusan sittin da uku; abin da ba zan iya tabbatarwa ba shi ne ko a cikin coci aka samu gawarwakin".

Ya kuma kara da cewa jimillar mutane tamanin da hudu ne suka rasa rayukansu.

Baya ga wadannan gawarwakin mutane tamanin da hudu farar hula da wadanda ake zargin mahara ne, kakakin rundunar tsaron ya kuma bayyana cewa akwai jami'an tsaro biyu da suka rasa rayukansu, ga kuma manyan 'yan siyasar da suka gamu da ajalinsu a sakamakon firgita bayan karar harbe-harben bindiga a kusa da inda suke halartar jana'izar mutane a yankin.

Manyan 'yan siyasar biyu da aka kashe dai su ne dan Majalisar Dattawan Najeriya, Gyang Dantong da Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokoki ta Jihar Filato, Gyang Fulani, wadanda 'yan kabilar Berom ne kuma 'yan jam'iyyar PDP mai mulki.

Hakazalika wadansu rahotanni sun bayyana cewa an samu asarar rayukan mutane akalla uku a yankin Heipang ranar Lahadi da maraice, ciki har da wani jami'in hukumar shige da fice ta Nijeriya; amma kakakin rundunar tsaron ya ce ba shi da tabbacin asarar rayuka ko da yake suna sane da cewa wadansu matasa da suka tare hanya sun kona motocin mutane a yankin.

Yanzu haka dai babban hafsan tsaron Najeriya, wanda tun watannin baya, gwamnatin kasar ta karbi ragamar tsaron jihar ta Filato ta mika masa da zimmar kawo karshen tashe-tashen hankulan, yana jihar inda wadansu majiyoyi suka ce yana ganawa da jami'an tsaro da sauran manyan masu ruwa-da-tsaki da nufin nemo mafita, yayin da a bangare guda kuma dokar hana fita daga karfe shida na yamma zuwa karfe goma sha biyu na rana ke ci gaba da aiki a yankunan kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Riyom da kuma Barikin Ladi.

Karin bayani