Sudan ta Kudu ta shekara guda da 'yancin kai

Sudan ta kudu: bukukuwan samun 'yan cin kai

Asalin hoton, INTERNET

Bayanan hoto,

Sudan ta kudu: bukukuwan samun 'yan cin kai

Yau shekara guda ke nan tun bayan da Sudan ta Kudu ta ayyana 'yancin kai bayan shafe shekaru da dama ana yaki tsakanin yankin da Sudan.

Ana dai bukukuwa a yau din a duk fadin kasar ta Sudan ta kudu.

Sai dai wannan shekara guda ta kasance mai cike da kulubale ga sabuwar kasar.

An yi ta fama da tashe-tashen hankula na kabilanci da kuma matsalar cin hanci da rashawa a sabuwar kasar ta Sudan ta Kudu.