Assad ba shi da niyyar sauka daga mulki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Syria Al Assad

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya sake bayyana cewar ba shi da niyyar sauka daga karagar mulki.

A wata hira da gidan talabijin na kasar Jamus, Mista Assad ya ce Syria tana fuskantar wani kalubale ne na kasa to amma bai kamata shugaba ya guje wa kalubaleb ba.

Ya zargi Amurka da laifin taimaka wa abin da ya kira gungun wasu mutane don a wargaza Syria.

Ya ce: "Amurka tana cikin masu haddasa rikicin. Sun ba da goyon baya na siyasa ga gungun wadannan mutane, domin su haddasa fitina - su wargaza Syria."

Shugaba Assad din zai yi wasu sababbin shawarwari a yau litinin da wakilin Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan wanda ya kai ziyara ta uku kenan a kasar Syria.

Karin bayani