Ana ci gaba da dambarwar siyasa a Masar

Zaman Majalisar Dokokin Masar Hakkin mallakar hoto s
Image caption Majalisar Dokokin Masar ta yi gajeren zama ranar Talata

Kotun kolin tsarin mulkin kasar Masar ta soke matakin da shugaba Mohammed Morsi ya dauka na maido da majalisar dokokin kasar.

A yau talata ne Majalisar ta yi zamanta duk da matakin da majalisar sojin kasar ta dauka wanda ya bada umarnin rusa ta bayan hukuncin da kotun tsarin mulkin ta yanke.

Sai dai kuma wasu kwararru ta fuskar shari'a a Masar din sun ce zaman majalisar na yau na iya mika ikon majalisar ga shugaba Morsi, wanda aka zaba cikin watan jiya.

Kuma wakiliyar BBC a birnin Alkahira ta ce gwagwarmayar iko tsakanin shugaba Morsi a bangare daya da kuma majalisar sojin da kotun kolin tsarin mulkin kasar a dayan bangaren za ta dauki watanni.