Talauci zai ragu a duniya da kusan rabi a 2025

Talauci zai ragu da kusan rabi nan da 2025
Image caption Talauci zai ragu da kusan rabi nan da 2025

Wata cibiya ta kasar Burtaniya da ke nazari a kan harkokin ci gaba mai suna Overseas Development Institute ta ce talauci ya ragu a duniya da rabi tun daga shekarar 1990 kuma zai sake raguwa da kusan rabi nan da shekara ta 2025.

Cibiyar ta ce ya zuwan wannan lokacin, yawan mutanen da ke rayuwa a cikin talauci zai yi kasa zuwa miliyan dari shida.

Cibiyar ta kuma ce wani labari mara dadin ji shi ne akasarin wadannan mutanen za su kasance ne a kasashen da ke fama da rikice-rikice irin su Najeriya, da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo da kuma Afghanistan.

Talauci a wadannan kasashen ya tsaya kusan inda ya ke ne tun shekarar 1990.