Sojojin Najeriya sun hakawa jama'a rijiya

Birgediya Janar Iliyasu Isa Abba
Image caption Kwamandan Birged ta uku a Kano, Birgediya Janar Iliyasu Isa Abba

A duk lokacin da aka ambaci soja dai abinda yake fara zuwa zukatan jama'a shi ne bindiga, yaki, rashin tausayi da muzurai.

Sai dai kuma Birged ta uku ta Rundunar Sojan Kasa ta Najeriya a Kano da ke arewacin kasar ta mika wadansu rijiyoyin tuka-tuka bakwai da ta ginawa wadansu al'ummomi a jihar.

A cewar Rundunar, an samar da rijiyoyin ne a wani bangare na ci gaba da bikin Ranar Sojoji ta kasar, da nufin kara kyautata alaka tsakanin sojojin da jama'a.

An dai gudanar da kwarya-kwaryan taron mika daya daga rijiyoyin ne a unguwar Kwanar Dala dake cikin birnin Kano.

A cewar kwamandan rundunar da ke Kano, Birgediya Janar Iliyasu Isa Abba, “Muna aiki ne saboda jama’a—idan kuma muan aiki saboda jama’a ne dole mu nemi goyon bayansu don mu cimma burin abin da ya kawo mu nan”.

Ya kuma ce suna fata da hakan za su kyautata alakarsu da jama’a wacce ta yi tsami.

Unguwar ta Kwanar Dala dai ta jima tana fama da karancin ruwa; wadansu mazauna unguwar sun bayyana irin wahalar da suke fuskanta ta ruwa da kuma yadda rijiyoyin za su agaza musu.

Wani mazaunin unguwar ya shaidawa BBC cewa “Rijiyoyin burtsatse—muna da guda biyu— akalla daga karfe goma sha biyu zuwa karfe biyu na dare ne za ka samu rangwamen mutane, kamar mutum biyar ko shida. Har kokawa,[kai] har kakkaryewa an yi a kan diban ruwan nan”.

Unguwar ta Kwanar Dala dai na ciki wuraren da aka taba samun asarar rai sakamakon aikin tsaro na rundunar hadin gwiwa a Kano, kuma a cewar wani mazaunin unguwar duk da cewa sun gode da rijiyar tuka-tukar da aka samar musu, har yanzu fa radadin abin da ya faru yana tare da su.

Rijiyoyi bakwai ne dai rundunar ta hakawa jama'a a unguwanni daban daban, kuma hafsan hafsoshin sojojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Ihejirika ne ya kaddamar da ta farko a unguwar Dabai a karshen watan jiya yayin wata ziyara da ya kai jihar ta Kano.