CAN ta yi kira ga Amurka a kan Boko Haram

Image caption Shugaban kungiyar CAN

Shugaban kungiyar mabiya addinin kirista a Najeriya, Pastor Ayo Oritsejafor ya yi kira ga majalisar dokokin Amurka da ta ayyana Kungiyar nan ta Jama'atu Ahlus Sunna Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Shugaban na CAN ya yi wannan kira ne a lokacin da ya bayyana a gaban 'yan majalisar dokokin domin ya yi bayani game da aikace aikacen 'yan kungiyar a Najeriya.

'Yan majalisar dokokin Amurkan da dama na jam'iyyar Republican sun soki Shugaba Barack Obama saboda rashin sanya sunan kungiyar a cikin kungiyoyin 'yan ta'adda na duniya.

Karin bayani