FIFA ta zargi Joao Havelange da almundahana

Havelange da tsohon surukinsa, Teixiera Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Havelange da tsohon surukinsa, Teixiera

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta fitar da wasu takardu dake cewa tsohon shugabanta, Joao Havelange da tsohon surikinsa, Ricardo Teixeira sun karbi wasu kudadan da suka saba doka.

Takardun sun nuna cewa tsakanin shekarar 1992 zuwa ta 2000, mutanen biyu sun karbi sama da dala miliyan ashirin da biyu daga tsohon kamfanin da hukumar FIFAN tai huldar kasuwanci da shi, wato ISL.

Wakiliyar BBC ta ce an ambaci sunan shugaban hukumar kwallon kafar mai ci, Sep Blatter a takardun, sai dai kuma ba a zarge shi da karbar cin hanci ba.

Fitar da takardun na zuwa ne jim kadan bayan da wata kotu a Switzerland ta umurci hukumar ta FIFA da ta fitar da sunayen jami'an dake da hannu a badakalar.

Kampanin na ISL dai ya durkushe ne a 2001.

Binciken da aka gudanar game da durkushewarsa ne ya bankado wannan lamari na cuwa cuwa.

Karin bayani