Burtaniya za ta baiwa kasashe matalauta da tallafin tsarin iyali

Contraceptive
Image caption Magungunan hana daukar ciki

Gwamnatin Birtaniya ta ce zata samar da fiye da dala billiyan biyu a cikin shekaru takwas don biyan kudin magungunan rage haihuwa a kasashe matalauta.

Za ta bayarda sanarwar alkawarin nata ne a wajen wani taro da za a gudanar a birnin London kan kayyade iyali wanda gwamnatin Birtaniyar tare da hadin gwiwar gidauniyar attajirin nan Bill Gates da uwar gidansa Malinda suka dauki nauyi shiryawa.

A wajen wannan taron wanda ke zuwa a daidai lokacin da bikin ranar yawan jama'a ta duniya ke mayar da hankalinsa kan yiwuwar samun hanyoyin kiwon lafiya da ake bukata ta fuskar yaduwar al'umma ana saran ita ma gidauniyar tayi alkawalin bayarda wata gudummuwar kudi mai tsoka.

Amma uwar gidan hamshakin attajirin Malinda Gates tace babban abinda ke gaban gidauniyar shine tallafawa gwamnatocin wajen aiwatar tsarin na kayyade iyali.