An kara rusa wasu hubarori 2 a Timbuktu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Ansar_ud_deen suna wata hubbare a Timbuktu

Mayaka masu kishin Islama sun sake ragar-gaza wasu karin hubbarori biyu a birnin Timbuktu na kasar Mali.

Kimanin mayaka goma sha biyu ne suka isa inda masallacin Djingareyber yake cikin wasu motocin a-kori-kura, inda suka harba bindigogi a sama don firgita mutane sa'annan suka fara aikin rurrusa hubbarorin.

A makon jiya ma an kai irin wadannan hare-hare kan wasu wuraren tarihi a Timbuktu.

Mayakan na Ansar-ud-dine dai sun lashi takobin lalata duk wani kabarinda aka kawata ta yadda aka sabawa dokokin addinin musulunci.

Karin bayani