Spain ta tsaurara tsuke bakin aljihu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Prim minista, Mario Rajoy

Pirayim Ministan Kasar S pain, Mariano Rajoy, ya bayyana wasu kwararan matakan tsuke bakin aljihu da suka hada da yin kari akan harajin sayar da kaya daga maki uku zuwa kashi ashirin da daya cikin dari.

Matakan tsuke bakin aljihun sun kuma hada da soke bayar da kudaden garabasa ga ma'aikata da yawa, sannan kuma za a zabtare albashi a kananan hukumomi da kusan kashi daya cikin uku.

Rage ragen na daga cikin wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma tare da shugabannin kasashe masu amfani da kudin Euro domin taimakawa farfado da bangaren Banki na kasar ta Spain.

Sanarwar ta Mr Rajoy ta yi gamkatar da wani maci a tsakiyar birnin Madrid da mahaka kwal dake zanga zanga ke yi.