Spain ta dauki matakan tsuke bakin aljihu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mariano Rajoy

Firayim Ministan Spain, Mariano Rajoy, ya bayar da sanarwar daukar wasu tsauraran matakan tsuke bakin aljihu, wadanda suka hada da kara harajin da masu saye da sayarwa ke biya da kashi uku cikin dari.

Kazalika za a daina bai wa ma'aikata da dama garabasar da a ke bayarwa lokacin kirsimeti, sannan kuma za a rage albashin kananan hukumomi da kusan kashi daya cikin uku.

Rage kudin dai wani bangarene na yarjejeniyar da suka kulla da shugabannin kasashen da ke amfani da kudin Euro don a taimaka a ceto bankunan kasar ta Spain.

Sanarwar ta Mista Rajoy ta zo a dai dai lokacin da ma'aikatan hakar ma'adanai na kasar ke wata zanga-zanga a tsakiyar birnin Madrid.

Rahotannin baya bayannan dai na cewa an yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da magoya bayansu da kuma 'yan sanda.

Karin bayani