An aike da karin dakaru zuwa Congo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojan Majalisar Dinkin Duniya a Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta aike da dakarunta zuwa Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo domin su kara karfafa kasancewarta a gabashin garin Goma dake fuskantar barazana daga 'yan tawaye.

Majalisar ta kuma jaddada cewa a shirye take ta kare al'ummomin yankin daga mayakan 'yan tawayen na M23.

A 'yan kwanakin baya dai an yi ta samun karuwar biranen da 'yan tawayen ke kwacewa, kuma yanzu suna dab da kwace birnin Goma dake gabascin kasar wanda shine babbar cibiyar yankin na gabashi.

A halin yanzu dai sojan gwamnati sun yi nasarar kwace garuruwan Rutshuru da Kiwanja daga hannun 'yan tawayen, sai dai kuma kamar yadda wakilin BBC Venuste Nshimiyimana ya bayyana, tarihi ne ke neman ya maimaita kansa.

Karin bayani