Hafsoshin sojin kasashen sahel na taro a kan Mali

Mali rebel Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawayen Mali

Manyan Hafsan sojojin kasashen Nijar, da Mali, da Mauritaniya, da Kuma Aljeriya na wani taro a birnin Nouakchott na Mauritaniya inda suke tattauna batun halin da ake ciki game da tabarbarewar sha'anin tsaro a yankin arewacin kasar Mali.

Jami'an soji dai musamman na duba yiwuwar amfani da karfin soja domin maido da zaman lafiya a wannan yankin da ke hannun 'yan tawaye tun cikin watan Afrilun da ya gabata.

Babban makasudin wannan taron wanda akeyi a asirce a babban birnin Mauritaniyar dai shine duba yadda za a taimakawa halattaciyar gwamnatin ta Mali ta kwato yankin arewacin kasar daga hannun 'yan tawaye.

A baya kasar ta Mali na daga cikin kasashen da ake koyi da su a yammacin Afrika wajen biyar tsarin dimokradiyya,amma daga farkon wannan shekarar ta fada cikin wani mummunan rikici sakamokon bullar 'yan tawaye a yankin arewacin da kuma juyin mulkin da sojojin kasar suka yiwa zababben shugabanta Ahmadou Toumane Toure a watan Maris.