Birtaniya ta kare sa sojoji aikin tsaro a Olympic

sojoji na aikin tsaro Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption sojoji na aikin tsaro

Gwamnatin Birtaniya ta tabbatar cewar za a tura karin sojoji dubu uku da dari biyar domin sa ido a kan shingayen hanyoyi, a lokacin wasannin Olympics da za a yi a London.

An yanke shawarar ne saboda wani kamfanin tsaro mai zaman kansa -- G-4S -- ya gaza daukar wadatattun ma'aikata cikin lokaci domin wasannin da ake shirin farawa a cikin makonni biyu masu zuwa. Ya kamata ne a ce kampanin ya samar da masu gadi dubu goma, a wuraren gasar Olympic.

Kampanin ya ce ya gaza samar da adadin ne a sakamakon irin jinkirin da aka rika samu wajen tantancewa da kuma binciken ma'aikatan tsaron.

Sakatariyar harkokin cikin gida ta Birtaniya , Theresa May, wadda ke jagorantar kwamitin tabbatar da tsaro a wasannin Olympic, ta bayyana ne a gaban majalisar dokoki domin bayyana dalilan da suka sa ala tilas aka bukaci aikin sojoji dubu uku da dari biyar a yanzu, dab da ana shirye shiryen bude gasar.

Karin bayani