Kasashen Yamma na neman a sakawa Syria takunkumi

Russian Ambassador to UN Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jekadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin yake nuna rashin amincewar kasar sa ga daukar mataki kan Syria.

Kasashen Yammacin duniya na rarraba wani daftari kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda ke neman a sanya wa'adi kwanakki 10 ga shugaban kasar Syria Bashar Al-Assad na ya daina amfani da karfin soji akan 'yan kasarsa, ko kuma ya fuskanci takunkumi.

Suna dai son wannan ya kasance wani bangare na wani kudurin majalisar da zai sabunta wa'adin aikin tawagar masu shiga tsakanin da ta aike da ita zuwa Syria, wadda wa'adin ta ke karewa a mako mai zuwa.

Sai dai tuni Rasha ta nuna adawa da hakan, abinda ya kara nuna yadda kan kasashen duniya ya rarrabu kan batun na Syria.

Itama dai Rashar ta rarraba nata daftarin kuduri dake bayarda shawarar tsawaita wa'adin zuwa kwanakki 90, tare baiwa tawagar karin damar taka rawa a siyasance tun da babu wata tsagaita wutar da zasu sanyawa ido.

Mai shiga tsakani

A wani jawabi da babban mai shiga tsakani a fadan na Syria Kofi Annan yayi wa kwamitin tsaron a kebance, yayi kira gareshi da ya aikewa gwamnati da kuma 'yan tawayen Syria da wani sako cewar akwai sakamako maras dadi idan suka ki tsagaita wuta; abin da Jekadun kasashen yammacin suka yi anfani dashi wajen kafa hujjar neman saka takunkumin. Amma Rasha ta kara nanata bukatar gwamnatoci masu karfin fada-aji da su hurawa 'yan adawa da kuma gwamnati wuta ta su amince da tsagaita wutar. Wakiliyar BBc a majalisar Barbara Plett tace a dai sani ba ko za a iya warware wadannan bambance- bambancen ko kuma daga karshe zasu kawarda duk damar da ake da ta+ sabunta wa'adin aikin tawagar majalisar dake Syria. Jami'an Majalisar dinkin duniya dai basu son ganin an rushe tagawar, inda suka ka ce yin hakan zai zama kamar Majalisar Dinkin Duniya ta fita batun Syria.