Maiduguri: bam ya kashe mutum biyar

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya 'yan sanda sun ce, akalla mutum biyar ne suka hallaka yayin wani harin kunar bakin wake a masallacin juma'a dake kusa da fadar shehun Barno.

Rahotanni dai na cewa, dan kunar bakin waken yayi kokarin kutsawa inda manyan jami'an gwamnati da suka hada da Shehun Barno suke kafin jami'an tsaro su gano shi.

Jihar Barno tana fama da tashin hankali tun daga shekara ta 2009 da rikici tsakanin hukumomi da 'yan kungiyar da ake kira Boko Haram ya kazanta.