Najeriya: matsalar inji ce ta haddasa hadarin jirgin Dana

Hadarin Jirgin saman Dana Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hadarin Jirgin saman Dana

Masu binciken hadarin jiragen sama a Najeriya sun ce matsalar inji ce ta haddasa faduwar jirgin saman Dana Air a Legas a watan jiya, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane 150.

A rahotonsu na wucin gadi, masu binciken sun ce direbobin jirgin sun ci karo da matsalar totur sannan kuma duka injinan jirgin biyu sun daina aiki a daidai lokacin da jirgin, wanda ya taso daga Abuja ya fara sauka a birnin na Legas.

Sai dai kuma Kwamihsina a hukumar binciken, Kyaftin Muktar Shu'aibu Usman, ya ce binciken bai kare ba:

Sai dai kuma rahoton ya musanta hasashen da ake yi cewa amfani da gurbataccaen mai ne ya sa injinan suka tsaya.

Karin bayani