'An yi kisan kiyashi a garin Hama na Syria'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani wurin da aka kaiwa harin bom a birnin Hama

'Yan adawa a kasar Syria sun ce dakarun gwamnati sun yi kisan kiyashi a tsakiyar yankin Hama.

Sun ce shaidu sun fada masu cewa, lamarin ya auku ne a kauyen Tremseh; inda aka hallaka mutane fiye da dari biyu.

Wasu rahotannin kuma na cewa mayakan kungiyar Shabbiha ne suka bude wuta a kauyen bayanda jirage masu saukar angulu suka yi ruwan bama bamai.

Kafar yada labarun gwamnati ta ce an yi taho mu gama ne tsakanin sojojin gwamnati da gungun masu dauke da makamai,inda wadanda ta kira 'yan ta'adda suka kwashi kashinsu a hannu.

Karin bayani