Kofi Annan ya nuna damuwa da kisan kiyashin da aka yi Syria

Kofi Annan Hakkin mallakar hoto s
Image caption Kofi Annan

Wakilin Majalisar dinkin duniya da kungiyar kasashen Larabawa ga Syria, Kofi Annan, ya ce ya kadu matuka, sannan ya kuma ji takaici gaya da jin rahotannin kisan kiyashin da aka yiwa jama'ar kauyen Tiremseh.

Tawagar majalisar dinkin duniya mai sa ido a kasar ta Syria ta ce tana kokarin tura jami'anta kauyen don su bincika kashe-kashen.

Shugaban tawagar, Manjo Janar Robert Mood, ya ce da zarar an samu tsagaita bude wuta za su je kauyen don ganewa idanonsu abin da ya faru.

Karin bayani