Amurka na daukar matakan kara takurawa Iran

Image caption Wata matatar mai a Iran

Baitil Malin Amurka ya fitarda sunayen karin wasu kanfunna da kuma daidaikun mutanen da zasu fuskanci takunkumin da ta sakawa Iran a halin yanzu.

Wannan bangare ne na wani kokarin da mahukumtan Washington keyi na ganin sun takurawa Tehran.

Baitil malin na Amurka yace kasar zata cigaba da takurawa Iran din har sai ta shawo kan damuwar da ake da ita game da shirinta na nukiliya.

Tarayyar Turai dai ta saka hani ga shigowa da man kasar Iran zuwa cikin yankunanta daga ranar daya ga wannan watan na Yuli inda ita kuwa Amurkar ta takaitawa manyan abokan huldar Iran adadin man za su iya saye daga gareta.

Kanfanonin da zasu fuskanci takunkumi

Baitil Malin dai ya fitarda sunayen kanfuna da Jiragen dakon mai da kuma bankuna gommai da yace na taimakwa Iran Karya takunkumin.

Mahukumtan a Washinton dai sun nuna jiragen ruwan dakon mai 58 na wani kanfanin jigilar mai, mai suna Iranian National Tanker Company mallakar gwamnati da kuma wasu kanfuna abokan cinakayyar wannan kanfanin su 27 wadanda gwamnati ke da iko da su.

Kanfanin dai ya sauya sunaye da tutocin jiragen nasa gabanin takunkumin ya soma aiki.

Baitil Mali ya samarda bayanai kan lambobin jiragen da kuma sabbin sunayen da aka chanza musu domin taimakawa kasashen duniya yin aikin da wannna takunkumin na tarayyar Turai da Amurka.

Hakama ya fitarda sunayen wasu daidai kun mutane da yace suna taimakawa kokarin da Iran keyi na samun fasahar kera makamin nukiliya.Sai dai Iran din ta nace kan cewar shirinta nukiliya na zaman lafiya ne.

Karin bayani