Najeriya: tanka ta yi barin bakin mai

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Rahotanni daga jihar Zamfara dake arewacin Najeriya na cewa, wata tanka ta yi barin bakin mai a cikin wani kogi dake kauyen Kadauri a karamar hukumar Maru.

Lamarin ya sa bakin mai ya malala a cikin kogin, kuma wasu na ganin hakan ka iya yin illa ga muhalli da kuma masu amfani da ruwan kogin.

Sai gwamnatin jihar Zamfaran tace, ta soma daukar mataki domin shawo kan lamarin, inda ta kuma ce zata nemi taimakon hukumomin da suka kamata wajen shawo kan lamarin.

Wannan dai ya faru ne kwana guda bayan hatsarin wata tankar mai ya kai ga hallaka mutane fiye da dari a kudancin Najeriya.