An kashe fitaccen dan siyasa a harin kunar-baki- wake a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani wurin da aka taba kai harin kunar bakin wake a Afghanistan

Wani dan kunar bakin wake ya halaka wani sanannen dan siyasa a Arewacin kasar Afghanistan, a lokacinda yake halartar wani daurin aure.

Wasu karin mutanen a kalla 20 sun rasu sakamakon bam din sannan wasu da dama kuma suka jikkata.

Dan siyasar wato Ahmad Khan Samangani ya rasu ne a lokacinda wani ya rungume shi a wurin bukin daurin auren, sannan ya tayarda bam din dake jikinsa lokacinda yake gaisawa da mutanen da suka zo bukin.

Wakilin BBC ya ce Samangani dan kabilar Uzbek, tsohon kwamanda ne na wasu mayakan sunkuru wanda ya ci gaba da jagorantar babbar rundunar mayaka har bayanda aka zabe shi a majalisar dokokin Afghanistan.

Karin bayani