Kungiyar CAN ta yi Allah-wadai da harin Maiduguri

Fadar Shehun Borno a Maidurguri Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fadar Shehun Borno a Maidurguri

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, wato CAN, Pastor Ayo Oritsejafor, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai a babban masallacin juma'a na birnin Maiduguri, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar da kuma jikkata wadansu—ciki har da sojoji biyu.

Da yake Allah-wadai da abin da ya kira “yunkuri a kan rayukan Shehun Borno, Alhaji Abukara Garbai El Knemi, da Mataimakain Gwamnan Jihar Borno a lokaci guda”, Pastor Oritsejiafor ya jajantawa gwamnati da mutanen jahar da kuma masarautar Borno da ma iyalan wadanda harin ya rusta da su.

Ayo Orsisejafar ya kuma baiwa Shehun na Borno da Mataimakin Gwamnan jihar shawara cewa kada harin ya girgiza su.

Daga nan ya bukaci Shehun da ya ci gaba da aiki don wanzar da zaman lafiya da hadin kan 'yan Najeriya.

Shugaban na CAN ya kuma yi kira ga masu fada-a-ji da su hada kai da gwamnati wajen kawo karshen zubar da jinni.

An kai harin ne dai jiya bayan sallar Juma'a, lokacin da Shehun na Borno da Mataimakin gwamnan ke fitowa daga Masallacin Juma’a.

Wadanda abin ya faru a gabansu dai sun ce dan kunar bakin waken yaro ne dan shekaru goma sha.

Karin bayani